in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashe-tashen hankali a Sudan ta Kudu ba su hana hakar man fetur ba
2013-12-23 14:18:22 cri

Jakadan kasar Sudan ta Kudu dake birnin Khartoum na kasar Sudan ya tabbatar a ranar Lahadi cewa, aikin hakar man fetur na kasarsa bai fuskanci matsala ba, sakamakon tashe-tashen hankali na baya baya, kana man fetur na cigaba da malala yadda ya kamata tun daga yankunan da ake hako shi zuwa bututuwan mai dake kasar Sudan.

A ko wace rana, Sudan ta Kudu na samar da gangar danyen mai dubu 250, in ji jakadan kasar Sudan ta Kudu dake kasar Sudan, mista Mayn Dot a yayin wani taron manema labarai.

Mista Dot ya bayyana cewa, har zuwa yanzu, wuraren hakar man fetur dake gabashin kasar ba su samu wata matsala ba, sakamakon tashe-tashen hankalin da suka faru a kasarsa, kuma rikicin siyasa ne ba wai rikicin kabilu ba ne.

Haka ya bayyana cewa, nan da 'yan makonni masu zuwa, gwamnatin Sudan ta Kudu za ta karbe ikon jihar Jonglei da ya tabbatar da cewa, a yanzu haka yana hannun sojojin dake biyayya tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu, Riek Machar.

A ranar 15 ga watan Disamban bara, munanan tashe-tashen hankali sun barke a Sudan ta Kudu tsakanin bangarorin sojojin kasar biyu, bangare guda na kabilar Dinka ta shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit yayin da bangare na kabilar Nuer ta mista Machar da ake zargi da neman hambarar da gwamnatin wannan kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China