in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kaddamar da wani shiri da zai kare fadawa yunwa a Mali
2014-02-28 10:02:55 cri

Ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai a Bamako, babban birnin kasar Mali a ranar Laraban nan ya kaddamar da wani shiri na shekaru biyu tsakanin wannan shekarar ta 2014 zuwa 2016 da zai fidda tsarin na musamman da a ganinsa zai yi maganin fuskantar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a kasar.

A bayanin babban jami'in mai kula da wannan aiki David Gressly, wannan shirin wanda babban makasudin shi shi ne a samar da hanyoyin da za'a bi domin kaucewa fuskantar yunwa da karancin abinci mai gina jiki zai bukaci a kalla kudi dala miliyan 568 a shekarar farko.

A cewar shi, kusan 'yan kasar 800,000 ne ke matukar fuskantar rashin tabbas game da samun abinci, kuma suna bukatar taimakon gaggawa na abinci sakamakon karanci amfanin gona, yanayin rikicin siyasa da ake fuskanta, da kuma talauci wanda ya rage adadin kayayyakin da ake sayarwa a kasuwanni.

Mr. David Gressly, lokacin da yake wa manema labarai bayani a Bamako, ya ce, domin ganin wadannan al'umma ba su galabaita ba kamar shekarar bara, akwai matukar bukata cikin gaggawa a taimaka wajen aikin noma a bana da kuma a badi.

Yankin arewacin Mali dai shi ne inda wannan matsala ta fi kamari ganin yadda mazauna ba su da hanyar samun agajin kiwon lafiya, abinci, ilimi, tsabtataccen ruwan sha da kuma yanayin muhalli mai kyau.

A wannan shekarar ta 2014, a bayanin Mr. Gressly, ma'aikatan ayyukan jin kai suna da shirin ganin a kalla kananan yara 639,000 a yankin kawai sun samu ilimi, tsabtataccen ruwan sha da kayayyakin kiwon lafiya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China