Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana matukar damuwa game da yanayin tsaron da ake ciki a arewacin kasar Mali, inda ya yi kira ga dukkan al'ummomin kasar da su tattauna a tsakaninsu yadda ya kamata.
Kwamitin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Alhamis, inda ya ce, irin abubuwan da suka rika faruwa a kasar, wata alama ce da ke nuna cewa, 'yan ta'adda da sauran kungiyoyi masu dauke da mamakai suna cin karensu ba babakka a kasar.
A saboda haka, kwamitin ya sake kira a bude kofar yin sulhu tsakanin dukkan al'ummomin arewacin kasar ta Mali, da nufin warware matsalar ta hanyar siyasa, ta yadda za a samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar cikin dogon lokaci.
Kwamitin ya kuma jaddada cewa, hakkin gwamnatin kasar Mali ce ta samar da zaman lafiya da tsaro a dukkan yankunanta. Sannan ya bukaci kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar, da su hanzarta ajiye makamansu su guji tayar da hankali.
Bugu da kari, kwamitin sulhun, ya yi kira ga dukkan bangarorin, da su amince da matakan da aka dauka na kwance damarar makaman kungiyoyin da ke dauke da makamai, a matsayin wani muhimmin mataki na kwance damara da shirin sake hada kan 'yan kasa bisa shirin samar da zaman lafiya.
Kwamitin ya yi maraba da shawarar da aka yanke a kwanakin baya wadda ta kai ga gudanar da zabe cikin nasara a ranar 24 ga watan Nuwamba da kuma ranar 15 ga watan Disamban bara, tare da yabawa hukumomi da al'ummar kasar ta Mali bisa halin dattakun da suka nuna. (Ibrahim)