Kakakin MDD Martin Nesirky ya tabbatar da cewa, ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na majalissar dinkin duniya 3 sun samu rauni lokacin wani hari da aka kai a arewacin kasar Mali a karshen makon da ya gabata.
Ma'aikatan suna binciken jerin fashe-fashen abubuwa ne da ya auku a jajibarin wannan rana kafin abkuwar wannan harin.
A ranar 14 ga watan Disamba da ya gabata ma sai da ma'aikatan wanzar da zaman lafiya 2 suka rasa rayukansu, wassu da dama kuma suka samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da aka kai a garin Kidal, babban birnin gundumar Kidal dake arewacin kasar, wanda ya zama cibiyar mafi yawan 'yan adawa daga kabilar Tuareg.
A ranar 25 ga watan Afrilun bara, kwamitin tsaro na MDD ya amince da kara yawan sojojin kiyaye zaman lafiya MINUSMA zuwa 12,600 domin su jagoranci sojojin kungiyar tarayyar kasashen Afrika dake Mali a ran 1 ga watan Yulin da ya gabata, tare da umartar sojojin da su yi amfani da dukkan hanyoyin da suka kamata wajen aiwatar da tsaro, kawo kwanciyar hankali, kare al'umma mazauna, ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD, kayayyakin tarihi, tare da taimaka wajen aikin jin kai. (Fatimah)