Magoya bayan kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin Islama a kasar Mali, sun lalata kimanin kaso 90 bisa dari, na kayayyakin tarihi, da suka wanzu tun karni na 11, a wurare daban daban, ciki hadda Gao Saneye dake arewacin kasar.
A cewar daraktan hukumar ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD UNESCO, mai kula da kasar ta Mali Lazare Eloundou Assomo, hakan ya auku ne a shekarar 2012, yayin da masu tsattsauran ra'ayi suka karbe ikon arewacin kasar.
Wani rahoto daga sashen lura da kayayyakin tarihin hukumar UNESCO, ya rawaito Assomo, na cewa, ziyarar gani da ido da ya kai, shi da sauran kwararru na kasa da kasa da wakilan gwamnatin Malin, ta ba su damar hasashen irin asarar da aka yi.
Assomo ya ce, kayayyakin kade-kade, da kayan ado irin na gargajiya, na cikin ababen da aka barnata, baya ga sashen wani masallacin dake Gao Saneye, da shi ma ke matukar bukatar gyare-gyare.
Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa, barnar da aka yiwa kayayyakin tarihi dake sassan birnin Timbuktu, sun haura abin da aka kiyasta a baya. Cikin wadannan kayayyaki, hadda sashen masallacin Djingareyber, da ya kasance daya daga shahararrun makarantun kowar da addini uku, da suka wanzu tun a karni na 15.
Rahoton ya ce, hukumar UNESCO za ta dauki matakan da suka wajaba,
wajen gyarawa, tare da kare daukacin kayayyakin tarihi da ke kasar ta Mali, a kokarinta na tabbatar da cewa, al'ummar kasar ba su yi asarar ababen tarihi da suka gada daga kaka da kakanni ba. (Saminu)