Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno dake tarayyar Najeriya, ya ce, harin da aka kai kauyen Izge, dake karamar hukumar Gwoza ba shi da wata alaka da wani addini.
Gwamna Shettima, wanda ya bayyana hakan yayin da yake jajantawa shugaban masarautar Gwoza Idrissa Timta, don gane da aukuwar lamarin, ya ce, musulmi ne ke da rinjaye a kauyen na Izge, don haka ba gaskiya ba ne zargin da ake yi cewa, Kiristoci aka kaiwa harin na ranar Asabar.
Gwamnan jihar ta Borno ya ce, kamata ya yi 'yan Najeriya su dauki kungiyar Boko Haram a matsayin wadda ke gaba da daukacin 'yan kasa, ba wai wani bangare na al'ummarta ba.
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin tarayya, da ta dauki sabbin matakan dakile ayyukan wannan kungiya, ganin irin ta'annatin da 'ya'yanta ke aiwatarwa, da kuma muggan makaman da suke amfani da su wajen karkashe al'umma.
Mutane 106 ne dai aka hallaka a daren ranar Asabar, baya ga wasu sojoji 9, da maharan kungiyar ta Boko Haram suka kashe da rana tsaka, kwanaki 3 kafin hakan a kauyen na Izge. (Saminu)