Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya, na cewa, kimanin mutane 50 ne ake kyautata tsammanin sun rasu, sakamakon farmakin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kaiwa kauyen Bama, na karamar hukumar Bama dake jihar.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, maharani cike da motoci, sun aukawa kauyen na Bama ne da misalin karfe 4 a asubahin ranar Laraba, suka kuma rika budewa mutane wuta tare da kone gidaje.
Wani wanda ya ganewa idonsa aukuwar lamari ya ce, kimanin gidaje 3000 ne maharani suka lalata.
Da yake tsokaci kan aukuwar wannan lamari, tsohon shugaban kungiyar 'yan kwadago ta Najeriyar Zanna Shettima, wanda 'dan asalin yankin na Bama ne, bayyana harin ya yi da mummunar ta'asa kan al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba. (Saminu)