Bayanai daga Najeriya na nuna cewa, a ranar Lahadi, wasu mahara sun kashe mutane a kalla 90 a jihar Borno da ta kasance tungar mayakan 'yan kungiyar Boko Haram da ke arewa maso gabashin kasar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Lawan Tanko, ya shaidawa manema labarai cewa, maharan sun dira wa kauyen Izge dake kudancin jihar da ke fama da tashin hankali a daren ranar Asabar, inda suka yi ta jefa bama-bamai kirar gida kan rufin kwanon gidajen mazauna wurin, kana bisani suka yi ta yin harbin kan mai uwa da wabi.
Ko da yake bai yi karin haske kan lamarin ba, amma sauran kafofin tsaro sun bayyana cewa, mutane kauyen sun gano gawawwaki 90, yayin da suke gudanar da aikin ceto a kauyen na Izge wanda ke makwabtaka da karamar hukumar Gwoza, da ita ma ta fuskanci kashe-kashen 'yan kungiyar a baya.
Jihar ta Borno wadda ke cikin jihohin kasar ta Najeriya da aka sanya wa dokar ta baci, ta kasance hedkwatar kungiyar Boko Haram da ta halaka dubban 'yan kasa da baki 'yan kasashen waje cikin shekaru 4 da rabi da ta kaddamar da hare-hare a kasar da ke yammacin Afirka.
A shekarar da ta gabata, gwamnatin Amurka, ta sanya kungiyar Boko Haram da ta Ansaru, cikin kungiyoyin ta'addaci da nufin taimakawa gwamnatin Najeriya dakile ayyukan kungiyar. (Ibrahim)