in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana zai halarci taro kan cutar Sida a birnin London
2014-02-13 11:02:58 cri

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya bar birnin Accra tun ranar jiya Laraba zuwa birnin London na kasar Ingila domin halartar taron da hukumar kula da shirin cutar Sida ta MDD UNAIDS da mujallar Lancet suka tsai da shiryawa ranar yau Alhamis.

Ana fatan dai wannan taro zai bayyana kokarin da kasa da kasa ke yi domin kawar da annobar HIV da Sida da kuma kyautata yanayin kiwon lafiya ta fuskar duniya. Wannan muhimmin taro na hadin gwiwa tsakanin hukumar MDD kan HIV da Sida da mujallar Lancet, wata manufa ce ta gamayyar kasa da kasa domin tashi tsaye wajen kare cigaban da aka samu har zuwa yanzu tun bayan shekaru da dama na yaki da wannan cuta.

Shugaban kasar Ghana zai yi kokarin aiwatar da nagartattun dabarun kasa da kasa domin kiyaye muhimman cigaban da aka samu, ta yadda za'a iyar shawo kan wannan annoba. A yayin wannan taro, manyan jami'an mujallar Lancet, darektan zartarwa na hukumar kula da ciwon Sida ta MDD Michel Sidibe, kwararru, wakilan bangarorin kiwon lafiya da kuma sauran masu ruwa da tsaki za su mai da hankali kan hanyar da kungiyar yaki da Sida ta duniya za ta iyar bi wajen zamanintar da ayyukanta domin cimma maradun kiwon lafiya na duniya cikin karko. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China