A gobe Juma'a ne ake sa ran kasashe 10 da kogin Nilu ya ratsa ta cikin su za su gana a kasar Uganda, domin tattauna hanyoyin bunkasa cin moriyar kogin ta fuskar samar da makamashin lantarki.
Karamar minista a ma'aikatar albarkatun ruwan kasar ta Uganda Betty Bigombe ce, ta bayyanawa manema labaru hakan a ranar Laraba.
Bigombe ta ce, za a yi amfani da zaman tattaunawar, wajen zakulo hanyoyin gudanar da hadin gwiwa karkashin babban shirin bunkasa makamashi na kasashe mambobin wannan yanki. Matakin da rashin daukar sa na iya dakile cimma cikakkiyar moriyar da ta dace kasashen su samu daga wannan kogi.
A cewar ministar, ganawar da kasashen za su yi a wannan karo, na cikin jerin shirye-shiryen tunawa da ranar da aka kebe domin wannan kogi, wanda kasashen dake makwaftaka da shi suka hada da Burundi, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Eritriya, da Habasha, da Kenya. Sauran su ne kasar Rwanda, da Sudan ta Kudu, da Sudan, Tanzania da kuma Uganda. (Saminu)