in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta taka muhimmiyar rawa a shawarwarin nukiliyar Iran
2014-02-19 17:56:02 cri

Shawarwarin da ke tsakanin kasashe shida da Iran kan maganar nukiliyar kasar ta Iran, na sabon zagaye an fara shi ne a ranar 18 ga wata da safe a birnin Vienna, babban birnin kasar Austria.

A wannan rana da safe, a matsayinta na mai kula da harkokin daidaita shawarwarin, wakiliyar kungiyar tarayyar Turai da ke kula da harkokin diplomasiyya da tsaro, Madam Catherine Ashton ta shugabanci cikakken zaman taron na farko, kuma tawagar kasar Iran da ke karkashin jagorancin Mohammed Javad Zarif, ministan harkokin wajen kasar, da ma wakilan kasashe shida mahalarta shawarwarin sun halarci taron. Michael Mann, kakakin madam Ashton a bayan taron ya bayyana wa manema labarai cewa, an fara shawarwarin ne a cikin yanayi mai kyau. A nasa bangaren kuma, Abbas Araqchi, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Iran ya amince da yanayi mai kyau da ya kasance wajen shawarwarin.

A watan Nuwamban da ya gabata ne, kasashe shida da batun nukiliyar Iran ya shafa da kuma kasar Iran din kanta suka cimma wata kwarya-kwaryar yarjejeniya dangane da yadda za a daidaita batun, yarjejeniyar da aka fara aiwatar da ita tun ranar 20 ga watan Janairun da ya gabata. Bisa yarjejeniyar, Iran ta daina tace sinadarin Uranium da ingancinsa ya kai sama da kashi 5%, har ma ta fara lalata wasu sinadarin da ta tace, a nasu bangaren kuma, Amurka da kungiyar tarayyar Turai sun fara janye takunkumin taba kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 4200 da Iran ta ajiye a wasu sassan ketare, abubuwan da suka share fagen shawarwarin na wannan zagaye. Michael Mann ya ce, babban makasudin da ake neman cimmawa a shawarwarin na wannan zagaye shi ne tabbatar da ajandar shawarwarin da za a yi a nan gaba, ya ce,"A gun shawarwarin, za a tattauna dukkanin abubuwan da ke shafar batun nukiliyar Iran, inda za a yi kokarin gano bakin zaren warwaren matsalar, don tabbatar da ganin ana gudanar da shirin nukiliyar Iran ne domin zaman lafiya. Za a yi kokarin tabbatar da tsarin shawarwarin da za a yi a nan gaba , ta yadda za a gudanar da shawarwarin da za a yi a nan gaba cikin sauki."

Kafin a fara shawarwarin, ministan harkokin waje na kasar Iran ya ce, za a iya cimma wata cikakkiyar yarjejeniyar da za ta daidaita batun nukiliyar Iran cikin wani wa'adi na watanni shida, duk da haka, ana ganin cewa, wannan ba abu ne mai sauki ba. A shawarwarin da za a gudanar a nan gaba, yadda za a sanya ido a kan hakkin Iran na mallakar nukiliya da kuma na'urorin nukiliya na kasar, su ne muhimman batutuwan da bangarori daban daban za su tattauna. A game da wannan, Michael Mann ya bayyana cewa, "Mun zo wajen shawarwarin ne tare da aminci, kuma mun zo nan tare da niyyar sa kaimin cimma wata yarjejeniya. Mun san matsalolin da muke fuskanta, amma Madam Ashton da wakilan kasashen shida za su yi kokarin sa kaimin cimma wata yarjejeniya.

Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin, Li Baodong a wannan rana ya bayyana cewa, batun nukiliyar Iran yana shafar zaman lafiya da tsaro a gabas ta tsakiya da kuma duniya baki daya. Yarjejeniyar da aka cimma a watan Nuwamba da ya gabata tsakanin kasashen shida da Iran wata muhimmiyar nasara ce, amma akwai sauran rina a kaba wajen daidaita batun kwata kwata. Li Baodong ya ce, dole ne bangarori daban daban su ci gaba da kokari bisa ga nasarar da aka samu, ya ce, "Idan ana fatan samun ci gaba mai muhimmanci, dole ne bangarori daban dadan su nuna niyya da jaruntaka, su bi hanyar yin shawarwari, don daidaita batun kamar yadda ya kamata. Domin cimma wannan buri, kasar Sin za ta ci gaba da ba da nata taimakon."

Za a shafe tsawon kwanaki uku ana shawarwarin na wannan zagaye, shawarwarin da za su kasance mataki na farko a kan hanyar cimma yarjejeniyar warware batun nukiliyar Iran kwata kwata. Idan mahalarta taron suka iya cimma daidaito a kan tsarin shawarwarin da za a yi a nan gaba da abubuwan da za a tattauna, za a iya cewa, sun shimfida harsashe ga shawarwarin da za a yi a gaba ke nan.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China