131016IrannukilyaAmi
|
Kasashe shida da batun nukiliyar Iran ya shafa ciki hadda Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin, Jamus da EU sun yi sabon shawarwari da Iran daga ran 15 zuwa 16 a birnin Geneva na kasar Switzerland. Wannan ya kasance karo na farko da suka yi shawarwari kan batun nukiliyar kasar ta Iran bayan kafa sabuwar gwamnatin kasar Iran a watan Agusta da ya gabata, inda bangarori daban-daban su ke nuna matukar taka tsan tsan a shawarwari wanda zai ingiza ci gaba da za a samu.
Kasashen shida da EU da kasar Iran sun kai ga cimma matsaya daya na yin shawawarin ne a karshen watan da ya gabata a birnin New York yayin babban taron MDD. Gwamnatin kasar Swiss ce ta jagoranci wannan shawarwari. Mahalartan taro sun hadda da ministan harkokin waje na kasar Iran Mohammad Javad Zarif, babbar jami'iyar EU mai kula da harkokin diplomasiyya da tsaro madam Catherine Ashton, mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Wendy Sherman, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Ryabkov da kuma manyan direktocin kula da harkokin siyasa na ma'aikatun harkokin waje na kasashen Birtaniya, Faransa, Jamus, yayin da kasar Sin kuma ta tura shugaban sashin kula da rundunar sojan kasar na ma'aikar harkokin wajen kasar Pang Sen.
Bayan isowarta birnin Geneva a ran Litinin 14 ga wata, madam Ashton ta ba da sanarwa a rubuce cewa, tana fatan za a samu ci gaba mai kyau a kwanaki biyu na shawarwarin, wanda ya kasance zarafi mai kyau game da samar da wata dama ga kasashen shida da EU na tattaunawa kan shawarar da muka gabatar wanda kuwa ya kasance burin kasar Iran. Ashton ta furta cewa, "muna matukar taka tsan-tsan domin samun ci gaba mai kyau a wannan karo. A hannu guda kuma, bayan wakilin kasar Iran Zarif ya isa Geneva, ya ce, yana fatan samun ganin kyakkyawar fata daga wajensu kan lamarin. Ban da haka, ya jaddada cewa, ba zai yiwu ba a warware matsala ta yin shawarwari guda daya kawai.
Bayan hawansa kan mukamin shugaban kasar Iran, Mr Hassan Rouhani ya dauki matakin da ya dace kan batun nukiliyar kasar. Yana mai cewa, za a yi kokarin warware rikici tsakanin Iran da kasashen yamma kan batun nukiliyar kasar. Bayan shawarwari da aka yi a karshen watan Satumba da ya gabata a birnin New York, sabon wakilin hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran ya yi shawarwari da wakilin IAEA, inda a wannan karo ake fatan tabo wasu hakikkanin batutuwa. Lamarin da ya nuna alamar cimma wani tudun dafawa kan wannan batu bayan shekaru goma da aka fuskanci matsala.
Duk da haka, warware wannan batu ta hanyar yin shawarwari ta shawarwari guda daya tilo ba zai yiwu ba. Ko za a samu ci gaba mai kyau ko a'a,hakan ya danganta da matakin da bangarorin biyu za su dauka na ja da baya da nuna hakuri. Wani babban batu dake jawo hankalin kasa da kasa shi ne, aikin tace Uranium da kasar ta Iran ke yi. An ba da labari cewa, Iran ta riga ta tace sinadarin Uranium mai ingancin da kashi 20% kimanin kilo 190, matakin da ake ganin zai baiwa kasar saukin harhada makaman nukiliya. Ban da dakatar da aikin tace Uranium, kasashen duniya sun nemi kasar ta Iran da ta daina jigilar Uranium da ta tace, kuma ta mika su ga wata kungiya. A nata bangare, kasar ta Iran ta nace ga ikon da ta ke da shi na yi amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, ba za ta ja da baya kan wannan batu ba ko kadan. An ba da labari cewa, watakila Iran za ta yarda ta ajiye sinadarin Uranium din da ta dace zuwa wuri mai nisa karkashin kulawar kasashen duniya. Wani batu na daban da zai jawo hankalin jama'a a yayin shawarwarin, shi ne bincike da za a yi kan na'u'rorinta na nukiliya, abin da ya sa kasar ta Iran ta gamu da suka daga kasashen duniya. Tun tuni, Iran za ta ki yarda da bukatun IAEA na yin bincike kan na'urori da shirin ta na nukiliya, a ganinta, wannan zai jawo illa ga tsaron kasar. Bisa labarin da aka bayar, Iran ta bayyana matsayin da ta dauka a Geneva, wato karin samar da haske kan aikin tace Uranium da ta yi domin neman kawar da wasu takunkumi da aka garkama mata, musamman ma hana ta fitar da man fetur dinta zuwa waje. (Amina)