A shirye take kasar Iran ta yi shawarwari a tsanake da kasashe shida
|
A yammacin ranar 6 ga wata a fadar shugaban kasa dake tsakiyar birnin Tehran na kasar Iran, shugaba Rouhani ya shirya taron manema labaru a karon farko tun da aka rantsar da shi, inda ya amsa tambayoyin manema labaru game da takaddamar da ke yi game da shirin nukiliyar Iran, yin tattaunawa da Amurka, takunkumi da kasashen yammacin duniya suka kakaba wa Iran, da kuma matsalar zaman rayuwar jama'ar kasar da sauransu.
Hassan Rouhani ya taba zama babban wakilin kasar Iran a shawarwarin da ake yi game da takaddamar nukiliyar kasar daga shekarar 2003 zuwa 2005, a lokacin ne Iran ta cimma yarjejeniya dangane da dakatar da ayyukan inganta sinadarin Uranium na dan lokaci tare da kasashe uku, ciki hadda Burtaniya, Faransa da Jamus. Bayan da Rouhani ya lashe zaben shugaban kasar Iran, bangarori daban daban na zura idon ganin yadda zai iya kawar da mawuyacin halin da ake ciki game da shawarwarin da ake yi kan shirin nukiliyar kasar.
Yayin da yake ba da amsa kan bambanci dake kasancewa tsakanin sabuwar gwamnati da ta da ta fuskar warware matsalar shirin nukiliyar kasar, Rouhani ya ce, shirin amfani da makamashin nukiliya ta hanyar lumana, wani batu ne dake shafar dukkan jam'iyyu da jama'ar kasar, saboda haka, dole ne a tsaya kan wasu manufofi,kuma sabuwar gwamnati ba za ta ba da kofa ba wajen kiyaye halaccin ikon kasar na amfani da makamashin nukiliya. Amma, a waje guda kuma a shirye sabuwar gwamnati take ta yi shawarwari mai ma'ana da bangarori daban daban, da nufin kawar da duk wata damuwa ba tare da bata lokaci ba.
"A matsayin na shugaban kasar Iran, ina shelanta a nan cewa, hakika jamhuriyar Islama ta kasar Iran na da niyyar warware takaddamar nukiliyar kasar a siyasance, yayin da take kokarin kare ikon jama'ar kasar, a sa'i daya tana la'akari da kawar da damuwar sauran kasashe. Muna fatan wadannan kasashe su ma na da irin wannan niyya, ta haka za a iya samu sakamako mai kyau cikin gajeren lokaci."
Rouhani ya kuma yi kira ga bangarori daban daban da batun ya shafa da su nuna tabbaci kan takkadamar nukiliyar Iran, kada su gabatar da bukatun da ba su dace ba, in ba haka ba, zai yi wuya a kawo karshen matsalar. Haka zalika ya jaddada cewa, kamata ya yi a warware matsalar ta hanyar tattaunawa, ba wai ta hanyar barazana ba.
Bayan an rantsar da Rouhani, fadar shugaban kasar Amurka, wato White Hous ta bayyana cewa, idan gwamnatin Rouhani ta yi wa duniya alkawari, to Amurka tana son yin zaman amana da hada kai da Iran. Amma, kwanan baya, majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da wata doka da nufin kara sanya takunkumi mai tsanani ga Iran, wato za a rage adadin man fetur ganguna miliyan 1 da Iran ke fitar wa a ko wace rana zuwa ketare.
Yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru, Rouhani ya kuma nuna cewa, akwai sabani game da bayanan da kasar Amurka ta bayar, wannan ya nuna cewa, ba ta fahimci tsarin siyasa da yanayin kasar Iran ba. Iran na mayar da hankali kan abubuwan da Amurka ke aikatawa, a maimakon abubuwan da ta fada.
"Ba na son ambatar ko akwai bambancin tsarin ayyuka asiri tsakanin gwamnatin kasar Amurka da majalisar wakilan kasar, ko a'a. Muna mayar da hankali kan hakikanin manufofinta. Idan Amurka ta nuna sahihanci, kuma bisa matsayin nuna girma juna da zaman daidai wa daida, to hanyar yin mu'ammala mai inganci a bude take tsakanin kasashen biyu."
Bayan haka kuma, Rouhani ya ce, gwamnatinsa za ta kula da hakikanan matakai da Amurka za ta dauka, idan akwai masu inganci da ma'ana, to Iran za ta ba da amsar da ta dace. Amma, alamun sabani da Amurka ta nuna a yanzu haka sun nuna rashin sahihancinta a fili.
Takunkumi masu tsanani da kasashen yammacin duniya suka sanya wa Iran sun yi babban illa ga tattalin arziki da zaman rayuwar jama'ar kasar. Game da batun, Rouhani ya yi bayani a gun taron manema labarun cewa,
"Sun ce wai sun sanya takunkumi ne domin hana ayyukan nukiliya da shirin makamai masu linzami na Iran, wannan ba hujja ba ce, su ma sun fahimci wannan sosai. Mu kan fuskanci wahalhalu da dama wajen biyan kudi don shigar da kayayyakin masarufi na amfanin yau da kullum ga jama'armu. A bayyane burinsu na saka takunkumi ba domin ayyukan nukiliya da makamai masu linzami ba,burin su shi ne su kuntatawa zaman rayuwar jama'a." (Bilkisu)