in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara gudanar da sabbin shawarwari kan matsalar nukiliyar kasar Iran
2013-11-21 16:36:09 cri

Kasar Iran, da sauran kasashe masu ruwa da tsaki kan batun nukiliyar kasar Iran su shida, sun fara gudanar da sabbin shawarwari dangane da batun nukiliyar kasar ta Iran a ranar 20 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland. Hakan kuwa ya biyo bayan shawarwarin da suka ci tura a karon da ya gabata. An ce wakilan kasashen Amurka, da Rasha, da Sin, da Faransa, da Ingila, da Jamus, da kuma Iran za su ci gaba da kokarinsu don ganin sun daddale yarjejeniya don gane da wannan batu.

Bayan shawarwarin da aka yi a ranar 9 ga watan da muke ciki, wadanda ba su kai ga cimma matsayar tsaida wata yarjejeniya ba, kasashen shida sun sake dukufa don ganin sun shawo kan matsalar nukiliyar ta Iran, Wadannan shawarwari sun zamo karo na uku da aka gudanar cikin makwanni biyar da suka gabata.

A ranar ta 20 ga wata, a matsayin jagora, babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro, Madam Catherine Ashton wadda ta halarci liyafar cin abincin rana tare da ministan harkokin waje, kuma wakilin farko kan tattaunawar nukiliyar kasar Iran Mohammad Javad Zarif, ta kuma gana da wakilan da suka zo daga kasashen shida.

A kuma daren wannan rana an shirya cikakken zaman taro karo na farko, inda Iran da kasashe shida dukkansu suka halarta. Kakakin Madam Ashton Michael Mann, ya gayawa manema labaru cewa, Madam Ashton ta zo wurin ne tare da niyyar kara samun ci gaba, kuma tana fatan za a rage bambancin ra'ayoyin dake tsakanin bangarorin daban daban.

'Muna tattauna kan wasu muhimman abubuwa, a zagayen da ya gabata, mun samu babban ci gaba, sai dai mun ci karo da wasu bambance bambance na ra'ayoyi, muna fatan za a iya rage iri wadannan bambance bambance a wannan karo.'

A halin yanzu, abin da ke teburin shawarwari shi ne, wani kwarya-kwaryan shiri na watanni shida. Idan bangarorin da abin ya shafa sun daddale yarjejeniya kan shi, hakan zai baiwa kasar Iran din damar samun sassauci na rage mata takunkumin dake kan ta. Hakana kasashen yamma za su ci gaba da nazarin sahihancin aniyar kasar ta Iran.

A cikin wannan wa'adi, Iran da kasashe shida, za su ci gaba da tattaunawa kan shiri mai zuwa wato shirin karshe. Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya bayyana a ranar ta 20 ga wata da dare cewa, kasar Amurka tana fatan za a daddale wata kwarya-kwaryar yarjejeniya, domin cimma wannan buri, za kuma a soke wasu takunkumin da aka sanya wa Iran din, amma bisa karamin mataki, wanda ba zai shafi muhimman abubuwa da suka hada da takunkumin sayar da man fetur, da kuma takunkumin da ya shafi fannin kudi ba.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, da ke shugabantar tawagar wakilai ta kasar, Mista Li Baodong ya bayyana a wannan rana cewa, a zagayen da ya gabata, bangarori daban daban na nuna matsayinsu cikin tsanaki. Ya ce dukkansu sun nuna burin su na amfani da matakan siyasa don daidaita matsalar nukiliyar kasar ta Iran. Ya ce bangarorin sun samu cimma wasu muhimman nasarori a fannoni da dama, kuma sun kai ga cimma ra'ayi guda a wasu fannoni, wanda hakan ya dasa wani tushe mai muhimmanci ga sabbin shawawarin da ake yi yanzu haka. Game da haka, ya ce,

'Muna son samu kyakkyawan sakamako, muna da sharudda masu kyau, kuma mun dauki burin siyasa. Muna fatan bangarori daban daban za su yi amfani da wannan dama da ke da ma'ana a tarihi, su nuna hikima a fannin siyasa, tare da nuna sahihiyar zuciya, su hada kansu, kuma kada a ja da baya, in dai ana fatan samun sakamako mai kyau, to ya kamata a yi kokari tare, a kara nuna saukin kai.

Rahotannin baya bayan nan na nuna cewa, tawagar wakilan kasar Sin, na son yin kokari tare da bangarori daban daban, don sa kaimi da samun kyakkyawan sakamako yayin shawarwarin na wannan zagaye.'

A halin yanzu, kasar Faransa ta gabatar da bukatu guda hudu a yayin shawarwarin, kuma Isra'ila na bukatar kasashen yamma, su kara sanya takunkumi kan kasar Iran, a wannan yanayin da ake ciki, ko za a iya samun sakamako ko a'a? Tambaya ce da kasashen duniya suka zura ido don ganin amsar ta.

Tuni dai ministan harkokin wajen kasar Iran Mista Zarif, ya riga ya bayyana a taron na Geneva cewa, shi da Madam Ashton za su ci gaba da tattaunawa kan cikakkun manufofin da suka danganci batutuwan da aka tattauna a ranar 21 ga wata.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China