An fara binciken dalilin faduwar jirgin saman Mozambique a hukunce, kuma ana sa ran sakamako zai fito nan da kwanaki 30 masu zuwa, in ji wani jami'in kasar Namibia a ranar Lahadin nan 1 ga wata.
Kenapeta Kauaria, mukaddashin sakataren din din din na ma'aikatar ayyuka da sufuri wanda ya sanar da hakan ga manema labarai ya ce, za'a yi jigilar sauran burbushin jirgin saman a filin saukan jiragen sama na Rundu da ke arewacin Namibiya domin cigaba da bincike.
Ya ce, ana fatan samun wani sakamako da kuma shawarwari game da hadarin jirgin saman da zaran an kammala binciken kuma aka tabbatar da dalilin faduwar jirgin.
Shi dai jirgin saman na kamfanin jiragen sama na Mozambique yana kan hanyarsa ne zuwa Luanda bayan ya taso daga Maputo zuwa Botswana da Namibia lokacin da ya fadi kuma dukkan mutane 34 dake cikin jirgin sun mutu kafin masu ba da agajin suka isa wurin a safiyar ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba a gandun daji dake arewacin kasar.
Ana ganin cewar, jirgin na tafiya ne bisa nisan kafa 38,000 lokacin da ya fara saukowa kasa har ya kai kafa 5,000 a cikin kowane minti daya ranar Jumma'a da yamma.
Fasinjojin dake cikin jirgin sun hada da 'yan Mozambique 10, 'yan Angola 9, 'yan Portugul 6, Basine 1, 'dan Brazil 1 da kuma Bafaranshe 1. (Fatimah)