in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta dauki alhakin kai hari kan cibiyar jami'an tsaro a Najeriya
2013-12-13 09:57:48 cri

Shugaban kungiyar nan ta Boko Haram Abubakar Shekau, ya ce, kungiyarsu ce ta kai harin ranar 2 ga watan Disambar nan, a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Wani faifan bidiyo na mintuna 19 da aka rabawa manema labarai, ya nuna wanda ke ikirarin shi ne shugaban kungiyar ta Boko Haram, na bayyana yadda magoya bayan kungiyar, suka kone wasu gine-gine tare da lalata wasu jiragen dake harabar sansanin sojin a garin Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno.

Tun da fari dai wata sanarwa da darakta mai lura da harkokin tsaro na rundunar sojin kasar Chris Olukolade ya fitar, ta ce, dakarun rundunar sun samu nasarar dakile harin na ran 2 ga wata. A hannu guda kuma rundunar ta tabbatar da harbe 'yan bindiga 24 yayin dauki ba dadin da ya auku tsakanin sojoji da maharan.

Rahotanni sun bayyana cewa, an lalata jiragen saman soji uku, da wasu jirage masu saukar ungulu guda biyu yayin wancan hari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China