Mambobin kwamitin tsaron MDD sun bayyyana amincewarsu, don gane da komawa teburin shawarwari, da sassan Sudan ta Kudu da ba sa ga maciji da juna suka yi.
Mambobin kwamitin tsaron wadanda suka bayyana hakan ta wata sanarwa a ranar Alhamis, sun yi kira ga tsagin gwamnatin kasar da na 'yan adawa, da su martaba dokar tsagaita wuta da aka cimma cikin watan da ya shude.
Sanarwar ta bayyana fatan kasancewar wannan zama dake gudana a Adis Ababa na kasar Habasha, ya kasance hanyar warware matsalar siyasar kasar, da inganta zaman lafiya, tare da cimma managarcin sulhu. Baya ga zakulo hanyoyin kandagarcin tashe-tashen hankula, masu alaka da kabilanci dake addabar kasar.
Har wa yau, kwamitin tsaron ya jinjinawa kungiyar bunkasa gabashin Afirka ta IGAD, don gane da irin rawar da take takawa yayin wannan tattaunawa a karo na biyu.
Daga nan sai kwamitin tsaron ya bukaci da a baiwa wadanda ke tsare, tare da wadanda a baya aka taba tsarewa, sakamakon rikicin kasar Sudan ta Kudun damar shiga shirin tattaunawar dake gudana, a wani yunkuri na ganin an baiwa daukacin masu ruwa da tsaki dama, ta ba da cikakkiyar gudummawarsu. (Saminu)