in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu shiga tsakani sun fara tattaunawa da bangarori masu fada da juna a Sudan ta Kudu
2014-02-13 10:44:43 cri

A birnin Adis Ababa na kasar Habasha, an sake kiran tattaunawar siyasar na kasar Sudan ta Kudu tsakanin gwamnati da kungiyar 'yan adawa a yammacin Talatan nan 12 ga wata na wani sabon zagayen da zai samar da yarjejeniyar siyasa tsakanin dukkan bangarori dake gaba da juna, inda ake ta ganawa tsakanin masu shiga tsakani da kuma mahalarta taron.

A cikin wata sanarwa daga kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika IGAD wadda ita ce ke shiga tsakani, ta ce, manzannin musamman na wannan kungiyar suna nan suna tattaunawa da bangarorin biyu da masu ruwa da tsaki.

Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillanci labarai na Xinhua cewar, an dawo da tattaunawar neman zaman lafiyar ne a Adis Ababa bayan da masu shiga tsakani suka tabbatar wa 'yan adawar cewa, manyan 'yan jam'iyyun siyasar da aka tsare, za'a bar su su halarci wannan taron na Adis Ababa.

Ana kyautata zaton dubban mutane sun halaka, wassu kusan 870,000 kuma sun tsere daga gidajensu, a cikinsu, 145,000 sun shiga kasashe makwabtansu, sannan 75,000 suka fake a sansanonin MDD dake kasar, tun lokacin da fada ya barke a tsakiyar watan Disambar bara tsakanin sojojin gwamnati magoya bayan shugaban kasar Salva Kiir Mayardit da kuma sojojin adawa magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China