in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dubban jama'a na kauracewa tashin hankalin da ke faruwa a CAR
2014-02-08 10:27:22 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta yi gargadin cewa, tashin hankalin da ke faruwa a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) ya tilastawa dubban jama'a kaura zuwa kasashe makwabta.

Wannan gargadi da hukumar ta yi, na zuwa ne, yayin da kotun hukunta masu aikata manyan laifuffuka ta duniya (ICC) ta bayyana shirye-shiryen gudanar da bincike game da zargin da ake yi na aikata laifuffukan yaki a mummun fadan kabilancin da ke faruwa a kasar.

Kakakin hukumar Fatoumata Lejeune-Kaba ta bayyana cewa, kimanin mutane 9,000 ne suka arce daga kasar zuwa kasar Kamaru da ke makwabtaka da ita, wannan ya kawo adadin 'yan gudun hijirar kasar sama da 20,000 da suka gudu zuwa kasar ta Kamaru tun lokacin da aka fara fada a kasar.

Ta ce, sabbin 'yan gudun hijirar sun shaidawa hukumar cewa, sun bar kasar ce saboda fadan da ke faruwa tsakanin tsoffin 'yan tawayen Seleka da mayakan anti Balaka a Bangui, babban birnin kasar, yayin wasu kuma suka gudu saboda yadda 'yan anti-Balaka ke kara nausawa zuwa yankunansu.

An yi kiyasin cewa, dubban mutane ne aka kashe a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kana mutane miliyan 2.2, wato rabin yawan al'ummar kasar suke bukatar agajin jin kai sakamakon fadan da ya barke tsakanin 'yan tawayen Seleka, galibinsu musulmi da kuma anti-Balaka, galibi Kiristoci a watan Disamban shekarar 2012, fadan da ya rikide zuwa na kabilanci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China