Ministocin tsaro daga yankin gabashin Afirka sun kare wata ganawa a birnin Nairobi inda suka sha alwashin inganta zaman lafiya da tabbatar da tsaro a yankin dake fama da rikici.
Ministocin sun gana ne a babban birnin kasar Kenya don tattauanawa kan dabaru da suka dace, da nufin bunkasa rundunar ko ta kwana ta Afirka (EASF) wadda kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta kafa da nufin bunkasa zaman lafiya da dorewa a yankin.
An gudanar da wannan taro ne bayan da shugabannin Afirka suka amince a cikin watan Aprilu cewa, za su kafa wata rundunar aikin ko ta kwana mai yawan dakaru 5500, domin ba da taimako a samu kawo karshen yaki da fadace-fadace na fararen hula a cikin nahiyar.
Shugabanni da jami'ai daga Djibouti, Habasha, Somaliya, Sudan, Comoros, Eritrea, Ruwanda, Madagascar, Kenya da Seychelles duka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 11 ga watan Aprilu a kasar Habasha, inda a cikinta aka fayyace manufofi da kuma tsarin dokoki na rundunar, gami da kafofinta na samun kudin kasafi da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 2.5 a kowace shekara.
EASF na daga cikin hukumomi guda biyar na rundunar ko ta kwana da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta bullo da su da nufin shawo kan fadace-fadace da kuma inganta zaman lafiya da tsaro a nahiyar. (Lami)