in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
M23 a DRC ta rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta
2013-12-13 10:27:40 cri

Mahukuntan a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC sun daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar 'yan tawayen M23.

Ana dai sa ran yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma a ranar Alhamis 12 ga watan nan a birnin Nairobin kasar Kenya, karkashin kudurin wanzar da zaman lafiya da tuni aka cimma a birnin Kampala, za ta kawo karshen dauki ba dadin da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun kungiyar ta M23 a kasar.

Wata sanarwar bayan taro da shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya fitar, ta bayyana cewa, yarjejeniyar da aka cimma a wannan karo, za ta ba da cikakkiyar damar daidaita al'amura a kasar. Haka zalika za ta ba da damar sauya matsayin kungiyar ta M23 zuwa halastacciyar jam'iyyar siyasa.

Ban da wannan, yajejeniyar ta tanaji aiwatar da shirin yafiya, da kwance damarar yaki ga 'ya'yan kungiyar, da sakin 'ya'yan kungiyar dake tsare, da mayar da masu gudun hijira yankunansu, da dai sauran matakan sulhu.

Ita dai kungiyar 'yan tawayen M23, ta kunshi dakaru masu adawa da gwamnatin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, ciki hadda sojojin gwamnatin da suka yi tawaye cikin watan Afirilun shekarar 2012. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China