Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, da ya shiga tsakani a fadace-fadacen da ke haddasa asarar rayukan tsakanin manoma da makiyaya a wasu sassan kasar.
Bugu da kari, majalisar ta bukaci shugaba Jonathan da ya kira taron masu ruwa da tsaki da zai kunshi shugabannin kabilu, ta yadda za a kawo karshen yawan fadace-fadacen da ke faruwa.
Bayanai na nuna cewa, sama da mutane 500 ne suka mutu a fadace-fadacen kabilanci daban-daban da suka faru a shiyyoyi 6 na kasar ta Najeriya a shekara ta 2013.
Majalisar ta gabatar da shawarar ce, sakamakon kudurin da dan majalisa Sunday Karimi da ke wakiltar mazabar arewa ta tsakiyar jihar Kogi ya gabatar, kudurin da ya samu amincewar majalisar baki daya.
Karimi ya shaidawa majalisar cewa, fada tsakanin manoma da makiyaya ya zama ruwan dare, inda a cikin kasa da kwanaki 30 aka halaka mutane sama da 100 wadanda ba su san hawa ba balle sauka. (Ibrahim)