in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun fara muhimmiyar tattaunawa ta shekara-shekara kan dangantakarsu
2013-07-11 10:30:09 cri

A ranar Laraba ne aka fara muhimmiyar tattaunawa jiko na biyar tsakanin kasashen Sin da Amurka kan muhimman batutuwa da tattalin arziki a birnin Washington na kasar Amurka.

A yayin zaman na kwanaki biyu, manyan jami'ai daga cibiyoyi da ma'aikatun gwamnati na kasashen biyu za su tattauna da kuma yin shawarwari kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi siyasa, tsaro, tattalin arziki da kuma kudade.

Wadanda suke wakilci na musamman ma shugaba kasar Sin Xi Jinping, wato mataimakin firaminista Wang Yang da kuma mamban harkar kasa Yang Jiechi, su ne za su jagoranci taron tare da wakilin shugabn Amurka Barack Obama, wato sakataren harkokin waje na kasar John Kerry da kuma sakataren baitulmali Jacob Lew.

Da yake jawabi yayin bude taron ranar Laraba, mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden ya lura cewa, kasashen biyu suna da batutuwa da ra'ayinsu ya banbanta kansu, to amma idan aka nuna gaskiya da kuma hangen nesa, za su samo mafita da ta dace wa kasashen nasu.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China