in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Palesdinu a Czech ya mutu sakamakon fashewar kundin adana
2014-01-02 12:19:52 cri

Jakadan al'ummar Palesdinu a kasar Czech Jamal Al Jamal ya mutu a jiya Laraba 1 ga wata sakamakon fashewar kundin adana muhimman abubuwa dake cikin gidansa wanda aka samu tangardar wajen amfani da shi kamar yadda bincike ya nuna tukun, in ji kakakin hukumar 'yan sandar kasar Andrea Zoulova.

Andrea Zoulova ta ce, wannan ko kusa ba harin ta'addanci ba ne, amma ana cigaba da bincike, kuma 'yan sanda na duba duk sauran hanyoyin da za su nuna dalilin wannan hadari.

Ta ce, kundin adanan ya lalace kwarai, abin dake nuna cewa, kariyar dake jikin kundin ne ya fashe.

Shugaban rundunar 'yan sandan kasar Martin Cervicek shi ma ya ce, ko kusa wannan fashewar ba ta yi kama da harin ta'addanci ba.

Babban likita a bangaren fida a asibitin sojoji dake garin Prague inda aka kai Jamal domin ceto ransa, Daniel Langer ya yi bayanin cewa, jakada Jamal ya samu rauni a kirjinsa, ciki da kuma kansa.

Jakadan Palesdinun Jamal Al Jamal dai ya fara aiki ne a hukumance a kasar Czech a ranar 11 ga watan Oktaban bara, kuma ya kaura zuwa sabon gidan da zai kafa ofishin jakadancin Palesdina ne a 'yan kwanakin da suka gabata. Wannan fashewa ba ta lalata wajen gidan ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China