Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya bukaci kasar Amurka, da ta kara kaimi wajen ba da gudummawar cimma daidaito, a shawarwarin wanzar da zaman lafiya da ake ci gaba da yi yanzu haka, tsakanin bangaren Falasdinawa da kuma wakilan kasar Isra'ila.
Wannan bukata ta Abbas, wadda ya gabatar a ranar Talata 17 ga watan nan, yayin ganawarsa da manzon kasar ta Amurka don gane da batun wanzar da zaman lafiya Martin Indyk, na zuwa ne daidai lokacin da wakilan Falasdinawan ke cewa, kawo yanzu, babu wani ci gaba da tattaunawar ta haifar.
Yayin wannnan tattaunawa tasu, an daddale tsare-tsaren yadda ganawar da shugaba Barack Obama, da takwaransa na Falasdinun Mahmoud Abbas za ta kasance a mako mai zuwa, gabanin babban taron MDD da za a gudananr a birnin New York.
A maimakon tattauna dukkanin muhimman batutuwan da suka dace, ciki hadda na siyasa, tsagin wakilan Isra'ila sun nace kan tattauna al'amuran da suka jibanci tsaro kadai, matakin da Falasdinawa ke ganin sam bai dace ba, in ji wakilan Palastinawa. (Saminu)