Rahotanni daga kasar Iraki sun bayyana cewa, a kalla mutane 40 sun rasa rayukansu, baya ga wasu 75 da suka ji raunuka, sakamakon wasu hare-haren da aka kaddamar a sassan kasar daban daban a jiya Alhamis.
Daya daga cikin wadannan hare-haren da aka kaddamar da bama-bamai, ya auku ne a lardin Diyala dake gabashin kasar, wanda kuma nan take ya hallaka mutane 25. Har ila yau wasu mutanen 6 sun riga mu gidan gaskiya, bayan da wasu bama-bamai da aka dasa a cikin wata mota, da kuma gefen hanya suka tarwatse, a yankin Amiriyah dake yammacin birnin Bagadaza.
Rahotanni da kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ya samu sun bayyana wasu karin hare-hare, da suka auku a sassan kasar daban daban a wannan rana ta 21 ga wata. Ciki hadda fashewar bama-bamai a yankunan Taji, da Kasra dake daf da arewacin birnin Bagadaza, da arewa maso gabashin Diyala, da kuma garin Buhruz.
An ce, yankin da ya fuskanci hari mafi muni shi ne Sa'diyah, inda wani bam mai nauyin gaske ya tashi a wata kasuwa, ya kuma hallaka mutane 25, tare da raunata wasu 45.
Rahotannin sun kuma bayyana cewa, wasu mahara sun harbe wasu fareren hula a yankunan sa'diyah, da Baiyaa.
Bisa kididdigar shirin tallafi na MDD dake kasar ta Iraki, a tsakanin watan Janairun da ya gabata zuwa watan Oktobar bana, akalla mutane 7,000 ne suka rasa rayukansu, baya ga wasu 16,000 da suka jikkata, sakamakon hare-haren kunar bakin wake, da bangarorin kasar da ba sa ga maciji da juna ke kaiwa junansu. (Saminu)