in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kula da jiragen saman Najeriya ta kammala binciken jirgin saman da ya yi hadari
2013-12-16 12:04:35 cri

Hukumar kula da jiragen sama ta kasar Najeriya a ranar Lahadi 15 ga wata ta sanar da kammala bincikenta a kan kamfanin jirgin saman Dana, in ji Mr. Fola Akinkuotu, babban direkta a hukumar wanda ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, ciki har da Xinhua, kamfanin dillancin labarai na kasar Sin.

Mr. Akinkuotu ya ce, sakamakon da aka samu bayan kammala binciken a ranar Jumm'a ya yi kyau, duk da cewa, aiki ne tukuru da ya bukaci kwararru, sannan aka yi shi a bayyane ba rufa rufa da aka aiwatar, tare da sashin fidda matakai na jirage na hukumar tare da abokan hulda na kasashen waje.

Ya ce, hukumar za ta gana da mahukuntan kamfanin jiragen saman na Dana domin sake nazarin ayyukansu game da wadanda aka rufe, sannan kuma za'a samu kwararru masu zaman kansu da za su ba da shawara kan lokacin da ya dace a maido da zirga-zirgan jiragen saman na Dana.

Makasudin wannan bincike wanda ake yi a duk shekara ga dukkan jiragen sama shi ne domin a tabbatar da lafiyarsu a sararin samaniya a kuma kauce wa duk wani cikas da za'a iya fuskanta, in ji Fola Akinkuotu. Hukumar dai ta dakatar da jirgin saman Dana a watan Oktoba domin gudanar da cikakken bincike a kanta a karo na uku, bayan da daya daga cikin jiragen saman kamfanin na Dana ya fadi, bayan minti biyar, ya sauka a filin jiragen sama a jihar Ikkon Nigeriya a shekarar bara, inda daukacin fasinjoji 163 har da ma'aikatan jirgin suka halaka.

Kwanaki biyu bayan hadarin, gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbe lasisin izinin gudanar da jigilar fasinja daga hannun kamfanin Dana ta kuma umurci kamfanin da ta biya diyya a kan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China