in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun jikkata a hare-haren da aka kai a kasar Iraki
2013-10-18 10:37:59 cri

Bangaren 'yan sanda na kasar Iraki ya bayyana cewa, a kalla mutane 59 ne suka mutu, kana wasu 196 suka jikkata a ranar Alhamis, a wasu hare-haren da aka kai a sassan kasar, ciki har da wasu bama-baman da aka dana a cikin motocin da suka yi sanadiyar rayukan mutane 40 a Bagadaza, babban birnin kasar.

Wata majiyar 'yan sanda ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, a kalla mutane 11 ne suka mutu, kana wasu 21 suka jikkata yayin da wasu bama-baman da aka dana a cikin mota suka tashi a kusa da wani dakin cin abinci a yankin Alwaya da ke tsakiyar birnin Bagadaza.

Har ila yau, majiyar ta ce, wasu mutane 10 sun halaka, kana 20 suka ji rauni yayin da wani bam din da aka dana a cikin mota ya tashi a yankin Husseiniyah da ke arewa maso gabashin birnin Bagadaza, yayin da wani bam din da shi ma aka dana a cikin wata mota a yankin Mamel da ke gabashin Bagadaza, ya halaka mutane 6 tare da jikkata wasu 15.

Bugu da kari wani farar hula ya rasa ransa, kana wasu mutane 7 sun jikkata, lokacin da wani bam din da aka dana a cikin wata mota ya tashi a yankin Baya da ke kudu maso yammacin birnin Bagadaza.

Wata majiyar 'yan sanda da ta bukaci a sakaye sunanta ta sanar cewa, a safiyar wannan rana, a akalla mutane 15 ne suka mutu, kana wasu 60 suka jikkata lokacin da wani 'dan kunar bakin wake ya tada bam din da ya dana a yankin Muwafaqiya, wani kauyen mabiya 'yan Shi'a dake kusa da Mosul, mai nisan kimanin kilomita 400 arewa da Bagadaza.

A cewar tawagar MDD da ke aikin bayar da taimako a kasar Iraki, kasar tana fuskantar tashin hankali a cikin 'yan shekarun nan, inda kusan aka halaka 'yan kasar ta Iraki 6,000, kana sama da mutane 14,000 suka jikkata daga watan Janairu zuwa Satumban wannan shekara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China