Kasar Nijar ta yanke shawarar jigilar danyen man fetur dinta ta hanyar bututun man dake ratsa kasar Chadi zuwa kasar Kamaru, a cewar wata majiya mai tushe a birnin Yamai.
Bisa sakamakon binciken na yiyuwar wannan aiki da kamfanin harkar man fetur na kasar Sin CNPC ya gabatar, da shawarar da ya bayar game da hanyar da ke bi ta kasar Chadi da Kamaru da sauransu, misali tashar ruwan Cotonou da ke ratsa Nijar da Benin,, gwamnatin Nijar ta amince da wannan zabin farko dake ganin ya cike da sauki da kuma riba bayan wani zaman taron ranar Jumma'a.
Haka kuma taron ministocin ya yanke shawarar cewa, zai mika wannan muhimmin aiki ga kamfanin da aka kafa bisa wannan dalili, kuma jarin gudanar da wannan aiki zai fito daga kasashen Nijar, Chadi, Kamaru, kasar Sin da 'yan kasuwa masu zaman kansu na wadannan kasashe.
An cimma wata yarjejeniya tsakanin ministocin man fetur na kasar Nijar da Kamaru tun ranar 30 ga watan Satumban da ya gabata a birnin Yaounde, inda aka tabbatar da matakan da suka shafi jigilar man fetur din kasar Nijar zuwa kasar Kamaru.
A halin yanzu, Nijar na samar da gangar danyen mai dubu 20 a kowace rana, a yayin da bukatun cikin gida aka kiyasta su zuwa gangar mai 7000.
A cewar hukumomin kasar Nijar, idan aka fara harkar man fetur a wasu sabbin wurare 59, Nijar na fatan cimma gangar mai biliyan daya, kuma zai kasance tsakanin gangar man fetur dubu 60 zuwa dubu 80 da za'a rika jigilarsu a kowace rana ta hanyar bututun Nijar-Chadi-Kamaru. (Maman Ada)