in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatan gidajen mai da kanikawa sun shiga yajin aiki a Afirka ta Kudu
2013-09-12 15:22:36 cri

Yajin aikin da ma'aikatan gidajen mai da kanikawa suka shiga a kasar Afirka ta Kudu, ya sake tsananta halin matsi da sashen sufurin kasar ke ciki.

Rahotanni daga Afirka ta Kudun na nuna cewa, ma'aikatan da harkar sufuri ke dogara kan ayyukansu, sun tsunduma yajin aikin ne tun daga ranar Litinin 9 ga wata, inda suke neman karin albashin da ya kai dalar Amurka 3 a ko wace sa'a, a dukkanin fannonin ayyukansu, da kuma irin wannan kari ga ma'aikatan da ke karbar albashin da ya kai Rand 6,000 a ko wane wata nan da shekara ta 2016.

Sai dai kamfanoni da masana'antun da wannan batu ya shafa sun yi watsi da wannan bukata.

Tuni dai tasirin wannan yajin aiki ya fara haifar da matsaloli ga dinbin al'ummar kasar, musamman wadanda ke bukatar man fetir domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Rahotannin sun kuma bayyana cewa, kalubalen da ake fuskanta ya fi tsananta a sashen ma'aikatun kira-kiran motoci, wanda yanzu haka ke kokarin sake farfadowa, bayan kammalar yajin aikin makwanni uku da ya fuskanta a baya bayan nan.

Da yake karin haske kan irin tasirin da yajin aiki na wannan lokaci ka iya haifarwa, shugaban kungiyar masana'antun kirar motoci na kasar ko NAAMSA a takaice, ya ce, yajin aikin, zai haifar da babban koma baya ga ayyukan masana'antun nan da karshen wannan mako da muke ciki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China