Mataimakin shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kuma shugaban ofishin kula da huldar kasa da kasa na jami'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS Wang Jiarui ya ce, kasar Sin a shirye take ta inganta dangantaka da kasar Chadi.
Mr. Wang ya bayyana hakan ne a ranar Laraban da ta gabata lokacin da ya gana da firaministan kasar Chadi, Kalzeubet Pahimi Deubet a N'Djamena, babban birnin kasar, yana mai cewa, Sin da Chadi sun rike dangantakar zumuncin dake tsakaninsu cikin yanayi mai kyau ta hanyar hadin gwiwwa a sassa daban daban, don haka akwai haske a nan gaba game da hulda tsakanin kasashen biyu. Don haka ya ce, JKS a shirye take ta yi musayar ra'ayi da jam'iyyar dake karagar mulkin kasar Chadi wato PSM domin karuwa da juna.
A nashi jawabin, firaminista Kalzeubet Pahimi Deubet shi kuma cewa, hadin gwiwwa tsakanin kasashen biyu ya samar da alfanu ta kowane fanni wanda za'a iya daukar sa a wani abin koyi na salon dangantaka tsakanin Sin da Afrika. Ya ce, Kasar Chadi a shirye take ta dauki darussa daga kasar Sin a fannin abubuwan da ta aiwatar wajen samun nasarorin da yanzu haka take alfahari da shi. (Fatimah)