Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya aikawa majalisar dattawan kasar sunayen mutane 12 domin neman amincewar nada su ministoci
Shugaban majalisaar dattawan kasar ta Najeriya David Mark ne ya tabbatar da hakan cikin wata wasika da ya karanta a kwaryar majalisar ranar Talata.
Bugu da kari, shugaba Jonathan ya aikawa majalisar dattawan wadda ta dawo daga hutun kirsimeti sunayen sabbin shugabannin rundunonin sojojin kasar da aka nada.
Sunayen da shugaban kasar ya gabatarwa majalisar da yake fatan za ta tantance kafin nada su mukaman ministocin, sun hada da Sanata Mohmmed wakil daga jihar Borno, Hajiya Jamila Salik da Jakada Aminu Wali, dukkan su daga jihar Kano da kuma Akon Eyakenyi daga jihar Akwa Ibom.
Sauran sun hada da Sanata Musiliu Obanikoro daga jihar Lagos, T.W. Danagogo daga jihar Rivers, Asabe Ahmed daga jihar Niger da Abduljelili Adesiyan daga jihar Osun.
Sai kuma Lawrencia Mallam daga jihar Kaduna, Janar Aliyu Gusau mai ritaya daga jihar Zamfara, tsohon gwamnan jihar Adamawa Mr Boni Haruna daga jihar Adamawa, da kuma Khaliru Alhassan daga jihar Sokoto.
A bangaren shugabannin rundunonin sojojin kasar kuwa, shugaba Jonathan ya ce, ya gabatar wa majalisar sunayen ne kamar yadda doka ta 18 karamin layi na layi cikin baka na dokar sojojin kasar ta tanada.
Shugabannin rundunonin sojojin kasar sun hada da Air Marshal Alex Badeh wanda aka nada a matsayin babban hafsan tsaron kasar, Manjo janar Kenneth Minimah, babban hafsan sojojin kasa da Rear Admiral Usman Jibrin, babban hafsan sojojin ruwa, sai kuma Air Vice Marshal Adesola Amosu, babban hafsan sojojin sama.
Idan ba a manta ba, a ranar 16 ga watan Janairu ne shugaba Jonathan ya sanar da nada sabbin shugabannin rundunonin sojojin kasar. (Ibrahim)