Game da ta'azzarar tashe-tashen hankula a kasar Afrika ta Tsakiya CAR, shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya yi amfani da jawabinsa na bikin sabuwar shekara na ranar 31 ga watan Disamba, domin nuna allawadai kan korafe-korafen da ake na cewa, kasarsa na tallafawa 'yan tawayen Seleke.
"Ina ja da kowa kuma ya kawo shaidar zarginsa ga gamayyar kasa da kasa." in ji shugaba Deby Itno.
A cewarsa, kasar Chadi kullum tana bayyana damuwarta kan halin da ake ciki a kasar CAR, kuma tun daga shekarar 1994, kasarsa ta fara samar da tallafin kayayyaki, fasaha da kudi ga wannan kasa makwabciya domin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar.
A yanzu haka sojojin kasar Chadi 800 suna cikin tawagar samar da zaman lafiya ta MDD a kasar Afrika ta Tsakiya wato MISCA.
Tun yau da 'yan makonni, 'yan kasar Chadi mabiya addinin islama da ma sojojin kasar Chadi na MISCA, suna fuskantar hare-hare daga bangaren dakarun sa kai mabiya addinin kirista da aka fi sani na Anti-Balaka, da ake zargin 'yan kasar Chadi da hada kai da tsoffin 'yan tawayen Seleka wajen hambarar da gwamnatin Francois Bozize a cikin watan Febrairun shekarar 2013.
Kasar Chadi ta fara kwashe daruruwan mutanen dake cikin tsaka mai wuya a kasar Afrika ta Tsakiya a ranar 22 ga watan Disamba tare da kafa shirin tsugunar da su a cikin kasarta tare da ba su taimakon da ya dace. (Maman Ada)