Manyan jami'an kungiyoyin ba da agaji na kasashen Cote d'Ivoire da Ghana sun kaddamar a ranar Laraba a birnin Abidjan da wani zaman taron shawarwari kan batun mayar da 'yan gudun hijirar kasar Cote d'Ivoire da suka samu mafaka a kasar Ghana tun bayan barkewar rikicin siyasa a wannan kasa dake yammacin Afrika.
A cewar babban jami'in kungiyar ba da taimako ga 'yan gudun hijira da wadanda ba su da asalin kasashensu (SAARA), Timothee Ezouan ya ce, wannan wani yunkuri ne na ba da kwarin gwiwa ga 'yan gudun hijirar kasar Cote d'Ivoire da su dawo gida bisa yardarsu, ta yadda za'a ingiza shirin dawowarsu.
Bisa 'yan kasar Cote d'Ivoire 8500 da suka samu mafaka a kasar Ghana, mutanen kalilan ne suka bukaci dawowa Cote d'Ivoire, in ji mista Ezouan.
Idan aka yi la'akari da furucin wannan jami'i, daidaituwar matsala a kasar Cote d'Ivoire za ta taimawa wajen shawo kan 'yan gudun hijirar dake kasar Ghana wajabcin dawowa kasarsu ba tare da fargaba ba.
Dukkan alkaluma na nuna komi na kyautatuwa, kasa ta kama hanyar bunkasuwa. Ya kamata su dawo su dauki wurinsu domin shirin sake gina kasar, in ji babban jami'in kungiyar SAARA.
Haka kuma mista Timothee Ezouan ya bukaci da a cigaba da karfafa matakan fadakar da 'yan gudun hijira domin samu sakamakon da ake bukata. (Maman Ada)