Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ya isa ranar Lahadi a birnin Nouakchott a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu bisa goron gayyatar shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz.
A tsawon wannan ziyara, shugaban kasar Nijar zai yi tattaunawa tare da manyan jami'an kasar, musamman da shugaba Ould Abdel Aziz.
Sannan kuma ya isa Nouadhibou, babban birnin tattalin arzikin kasar dake da tazarar kilomita 450 daga arewacin birnin Nouakchott, inda zai ziyarci wasu manyan cibiyoyin hidimar wannan birnin dake bakin ruwa da aka mayar "yankin 'yancin yin musanya" ba da jimawa ba.
Shugaban kasar Nijar ya isa kasar ta Mauritania tare da wata babbar tawagar dake kunshe da wasu ministocin kasarsa.
Nijar da Mauritania, kasashe ne na yammacin Afrika da yankin Sahel dake fama da tashe-tashen hankali a halin yanzu sakamakon yakin da ake yi da kungiyoyin ta'adanci a arewacin kasar Mali. Kuma cikin wadannan kasashe biyu ne dai kungiyoyin kishin Islama dake alaka da kungiyar Al-Qaida a yankin Magreb wato AQMI suka sace wasu 'yan kasashen yammacin duniya. (Maman Ada)