in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya jaddada kirar kasar ta warware rikicin Sudan ta Kudu ta hanyar zaman lafiya
2014-01-16 10:38:04 cri

Jakadan kasar Sin a kasar Habasha Xie Xiaoyan a ranar Laraban nan ya sake jaddada kirar da kasar ke yi ta warware rikicin kasar Sudan ta Kudu ta hanyar zaman lafiya.

Mr. Xie wanda kuma shi ne wakilin kasar Sin a kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, yana bayani ne ga manema labarai a cibiyar kungiyar dake birnin Adis Ababa, inda ya kara bayyana gudumuwar da kasar Sin ke bayar domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar baki daya.

Jakadan ya jaddada bukatar dake akwai ga bangarori biyu dake arangama da juna a kasar ta Sudan ta Kudu da su warware rashin fahimtar dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da neman sulhu cikin lumana.

Yanzu haka tawaga daga gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da ta 'yan adawa suna ci gaba da tattaunawa a birnin Adis Ababa a karkashin shiga tsakanin kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka IGAD.

Mr. Xie ya tunatar da damuwar kasar Sin a kan zaman lafiya da tsaro a nahiyar a Afrika, inda ya ce, lokacin da ministan harkokin wajen kasar Sin ya ziyarci kasar Habasha kwanan nan, ya gana da tawagogin biyu, inda ya nuna cewa, Sin tana son ta ba da gudumuwarta wajen samar da zaman lafiya a wannan nahiyar.

Ya kuma lura nuna cewa, Sin ita ma tana bukatar ganin an dakatar da bude wuta nan take a kasar ta Sudan ta Kudu don kawo karshen tashin hankalin da al'umma ke fuskanta, yana mai jaddada cewa, ta hanyar tattaunawa da sulhu ne kawai kasar za ta maido da doka da oda yadda ya kamata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China