A ranar Litinin, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya jadadda muhimmancin yin hadin kai wajen tinkarar kalubale na duniya yayin bukin kiyaye ranar jin kan bil adama don martaba masu ayyukan tallafawa bil adama da suka rasa rayukansu a kan wannan aiki.
A cikin sakonsa, Mr. Ban ya ce, 'Muna tunowa da sadaukar da rayukansu da kuma sake jadadda dukufarsu kan ayyukan ceton bil adama da suke gudanarwa a fadin duniya, kuma a kullum, mafi yawan lokuta ma a cikin mawuyaci, da hali mai tsanani, wanda ba kowa ne zai iya ba, ko kuma ya so zuwa ba.'
A bukin na bana, MDD ta kaddamar da gangamin wayar da kai na fadin duniya mai take 'Duniya na bukatar kari' wadda ke da nufin jan hankulan jama'a su tallafawa al'umomi da suka shiga bala'i. Kamfen har wa yau yana so manyan cibiyoyi na duniya su dau nauyin kalma guda daya wacce a ganinsu tana da tasiri ga duniya.
A cikin sakon nasa, magatakardan ya zabi kalmar 'hadin gwiwa' inda ya ce, a lokacin da ake fuskantar kalubale, jama'a da kasashe na bukatar hada gwiwa domin cimma adalci, zaman lafiya, mutunci da kuma bunkasa.
A shekarar 2008 ne MDD ta ware ranar 19 ga watan Agustan kowace shekara a matsayin ranar jin kan bil adama ta duniya domin tunowa da tashin bam a otal din Canal a birnin Bagadaza na kasar Iraki a shekarar 2003 inda rayukan ma'aikatan MDD 22 suka salwanta, ciki har da jakadan MDD a Iraki Sergio Vieira De Mello, kana sama da 150 suka ji rauni.
An tanadi wasu harkokin kiyaye bukin ranar Litinin. Tun da farko, magatakardan MDD ya ajiye furanni a a hedkwatar MDD dake birnin New York don martaba ma'aikatan MDD da aka kashe a harin 'yan ta'adda a otal din Canal, inda nan ne hedkwatar MDD a kasar Iraki take shekaru 10 da suka wuce. (Lami)