Wani taron kwamitin kwararrun kasuwanci, kwastan da 'yancin zirga-zirga a cikin kungiyar tattalin arzikin yammancin kasashen Afrika (ECOWAS) ya bude a ranar Litinin a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire domin shirin fara amfanin katin 'dan kasa dake fayyace fasalin mutum, ta yadda za'a taimakawa al'ummomin kasashe mambobi yin zirga-zirga a wannan shiyya cikin walwala. A yayin wannan zaman taro na Abidjan kan yiyuwar sake nazari kan wasu matakai na huldarmu domin sanya wannan fasahar katin 'dan kasa, ta yadda za'a soke katin wucin gadi da wa'adin kwanaki 90 ga jama'ar kasashen, in ji shugaban taro mista Sanoh N'Faly, darektan zirga-zirga cikin 'yanci a kwamitin ECOWAS a cikin jawabinsa na bude taron. (Maman Ada)