Khartoum ta jaddada muhimmancin ziyarar da ake sa ran shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir zai kai a kasar Sudan ta Kudu a ranar Talatan nan mai zuwa, a cewar ministan harkokin kasashen wajen Sudan Ali Karti kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan SUNA ta bayyana.
Mr. Karti wanda ya yi bayanin cewa ziyarar ta biyo bayan gayyatar da shugaban kasar Sudan ta Kudun Salva Kiir Mayardit ya yi wa shugaba al-Bashir, ya ce, wannan ziyarar za ta ba da kafar da shugabannin biyu za su tattauna batutuwa da suka shafi yankin Abyei da kuma shawarar da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yanke game da batun, sannan kuma da matsayin da su shugabannin suka dauka game da hakan, hade da sauran batutuwa da suka shafi tafiyar da yarjejeniyar da aka cimma a baya.
Ministan harkokin wajen na Sudan ya kuma bayyana cewa, shugabannin biyu za su yi aiki tare don ganin batun Abyei ba zai kawo cikas ga cigaban da aka samu ya zuwa yanzu ba tsakanin kasashen biyu. Haka kuma za'a tattauna batun hulda a fannin ciniki da tattalin arziki gami da batun mai da kuma tsaro. (Fatimah)