in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 44 suka mutu a Iraki sakamakon tashin hankali
2013-09-16 15:18:26 cri

Majiyoyin 'yan sanda a kasar Iraki na bayyana cewa, a kalla mutane 44 ne suka mutu, kana wasu 133 suka jikkata sakamakon wasu hare-hare da aka kai a sassa daban-daban na kasar a ranar Lahadi.

Tun da farko a wannan rana, mutane 31 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 95 suka jikkata a sassa daban-daban na kasar sakamakon wasu jerin hare-haren bama-bamai, ciki har da hare-haren bama-baman da aka dasa a cikin motoci har sau 12 a lardunan da ke kudancin kasar, galibi na mabiya 'yan darikar Shi'a.

Sai dai ya zuwa yanzu, babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare, amma galibi reshen kungiyar al-Qaida da ke Iraki ne ke kaddamar da irin wadannan hare-haren bama-bamai.

A 'yan shekarun nan, kasar Iraki ta sha fuskantar tashe-tashen hankula, kuma a cewar MDD, sama da mutane 4,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare tun a watan Afrilu, ciki har da mutane 804 da suka mutu a watan Agusta kadai.

Bayanai na nuna cewa, babu wata doka da aka kaddamar, tun lokacin zabukan majalisar dokokin kasar a watan Maris na shekarar 2010. Ana fargabar cewa, kasar tana iya fada wa yakin basasa kamar na shekarar 2006 da ta 2007, inda adadin mutanen da ke mutuwa a ko wane wata ya zarce 3,000. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China