in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kwamitin jituwa na kasashe 5 kan zaman lafiya da cigaba a Yamai na Nijar
2013-12-18 12:21:22 cri

Babban birnin kasar Nijar, Yamai ya karbi bakuncin zaman taro a ranar Talata da safe na shugabannin kasashe 5 na mambobin kwamitin jituwa bisa taken karfafa zaman lafiya da samun cigaba.

Taron na birnin Yamai dake karkashin jagorancin shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, ya samu halartar takwarorinsa da suka hada Boni Yayi na kasar Benin, Blaise Compaore na Burkina Faso, Alhassan Dramane Ouattara na Cote d'Ivoire, Faure Gnassigbe na Togo, faraministan kasar Mali Omar Tatam Ly a matsayin 'dan kallo da sauran manyan baki.

Taron dai ya zo daidai lokacin da kwamitin jituwa na kasashe 5 ya fara aikin neman kawo muhimman sauye-sauye da za su baiwa kwamitin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata bisa manufar neman dunkulewar mambobin kasashensa da cigaban tattalin arzikinsu.

A yayin wannan zaman taro, shugabannin kasashe da gwamntoci za su rattaba hannu kan jadawalin aiki na shekarar 2013 zuwa shekarar 2016 na kwamitinsu da bullo da wasu hanyoyin samar da kudin aikinsa, duba jadawalin aikin shekarar 2014 da tattauna batutuwan tsaro na shiyyar domin samar da wani yankin da zai kasance wani ginshikin bunkasa tattalin arziki da ayyuka na gaba.

Haka kuma mahalartan taron za su mai da hankali kan shirin kafa wani layin dogo da zai ratsa manyan biranen kasashe mambobin kwamitin wato Lome, Cotonou, Niamey, Ouagadougou, Abidjan, ta yadda za'a iyar taimakawa hanyoyin samar da ruwa da makamashi a yankunan karkara na kwamitin.

An kafa kwamitin jituwa na kasashe 5 a shekarar 1959, bisa manufar bunkasa tattalin arzikin wadannan kasashe da suke hada da Benin, Nijar, Burkina Faso, Cote d'Ivoire da Togo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China