A ranar Litinin 11 ga wata ne al'ummar Palasdinawa ke bikin cika shekaru 9 da rasuwar tsohon jagoransu Yasser Arafat, inda jami'ai suka yi kiran da a gabatar da batun mutuwar tasa ga babban taron MDD.
Nasser al-Qudwa, 'dan uwa ga marigayi Arafat, ya shaidawa taron manema labarai cewa, matakin gabatar da batun mutuwar Arafat ga babban taron MDD, zai taimaka wajen share hanyar tuhumar Isra'ila da kashe Arafat, kana zai taimaka wajen samun yin allawadai daga kasashen duniya kan aikata wannan danyen aiki.
A makon da ya gabata ne, gidan talabijin na al-Jazeera mai mazauni a Qatar, ya bayar da rahoton cewa, kwararrun kasar Switzerland da suka gudanar da bincike kan gawar marigayin, sun gano sinadarin Polonium da ya ninka har sau 18, suna masu bayyana tabbacin kashi 83 cikin 100 cewa, an sanya wa Arafat din guba ne. (Ibrahim)