Rahotanni daga birnin Kudus na cewa, tattaunawar da wakilan Isra'ila, da na al'ummar Falasdinawa ke yi na fuskantar tarin matsalolin rashin cimma daidaito.
Wani jami'in al'ummar Falasdinu da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua cewa, fannin tsaron yankunan biyu ne ya fi fuskantar tirjiya. Jami'in ya kuma kara da cewa, ko a ranar Litinin sai da mahukuntan Isra'ila suka nuna rashin amincewa da wani jawabi, wanda shugaban al'ummar Falasdinu Mahmoud Abbas ya yi ta wata kafar talabijin, don gane da batun na tsaro, suna masu cewa, batun na tsaro, ba abu ne da bangare guda zai yanke hukunci a kansa ba.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Mahmoud Abbas ya bayyana cewa, wajibi ne a nan gaba harkar tsaron Falasdinu, ta zama karkashin kulawar al'ummarta, kuma Falasdinawa ba za su ki amincewa da samar da jami'an tsaron kasa da kasa na wucin gadi a kan iyakokinta ba.
Kawo yanzu dai wakilan bangarorin biyu na ci gaba da tattaunawa ne da nufin warware tarin matsalolin da suka hana samun cikakken yanayin zaman lafiya a tsakaninsu, tun bayan da suka gudanar da taron farko a birnin Washington na kasar Amurka, a karshen watan Yulin da ya gabata. Ko da yake dai da dama daga wakilan bangarorin biyu na ganin kawo yanzu ba a tsinana wani abin a-zo-a-gani ba. (Saminu)