Mutanen kasar Chadi sun gudanar a ranar Lahadi da wani yinin zaman makoki domin martaba wadanda suka kwata dama na hadadin jirgin ruwa na tsibirin Lampedusa na kasar Italiya bisa wani kudurin da shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya sanya wa hannu. An sauko da tutocin kasar kasa a dukkan fadin kasar da kuma hana duk wasu bukukuwa na bidi'a. Haka ma kafofin rediyo da talabijin na kasar sun dakakar da wasu shirye-shiryensu da suka saba yi domin watsa wakokin addini.
A cikin masallatai da cocinan N'Djamena, babban birnin kasar Chadi, fastoci da fada tare da limamai sun kebe wasu lokuta na yin adu'o'i ga 'yan ci ranin Afrika da suka mutu a teku a yayin da suke kokarin zuwa kasashen Turai.
A farkon watan Oktoba, fiye da bakin haure 'yan Afrika 360 da yawancinsu 'yan kasar Eritoria suka mutu ko suka bata a cikin hadarin jirgin ruwan da ya faru a gabar tsibirin Italiya. Fiye da dubu ishirin 'yan ci rani suka mutu a yayin da suka kokarin cimma burin zuwa shiyyar Turai a tsawon shekaru ishirin da suka gabata, a cewar wasu alkaluman hukumar ci ranin kasa da kasa ta (OIM).
A makon da ya gabata ma, kusan 'yan ci rani na kasar Nijar 92 yawanci mata da yara suka mutu dalilin kishi a cikin hamada a lokacin da suke kokarin isa kasar Aljeriya. A cikin wata wasika da ya aika wa takwaransa na kasar Nijar Mahamadou Issoufou a ranar Asabar, shugaban kasar Chadi ya jajantawa gwamnatin Nijar da kuma iyalan wadanda suka mutu da sunan al'ummar kasar Chadi. (Maman Ada)