in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na shirya wani taron kwararru kan sake gina kasar Somaliya
2013-08-28 10:57:11 cri

A ranar Talata a birnin Addis Abeba, kwamitin dake kula da harkokin tattalin arziki na MDD na shiyyar Afrika ya bude wani zaman taron kwararrun kasa da kasa na kwanaki uku da zai taimaka wajen bullo hanyoyi da dabarun cigaba da gine-gine da kafa nagartattun huhumomi a kasar Somaliya bayan da kasar ta fi fama da yake-yake a tsawon shekaru da dama. Wannan taro na hadin gwiwa tare da cibiyar nazarin tattalin arziki da zaman al'umma ta Horn (HESPI), wato wata cibiyar nazarin Afrika, ya tattara manyan ma'aikata da malaman jami'a na kasar Somaliya. Darektan janar na cibiyar HESPI, Ali Issa Abdi ya bayyana wa 'yan jarida cewa, wannan dandali na da manufar hada dukkan taimakon da gamayyar kasa da kasa take samarwa domin sake gina kasar Somaliya da kuma taimakawa wajen karfafa huhumomin kasar yadda ya kamata.

Baya ga taimakon da ya kamata gamayyar kasa da kasa ta kawo ta fuskar kudi, haka zalika ya kamata ta ba da taimakon kimiyya da fasaha domin taimakawa kasar Somaliya wajen sake gina manyan gine-ginen more rayuwar jama'a da na hukumomin kasar, in ji mista Abdi.

Kasar Somaliya a yanzu tana bukatar samun kulawa da taimako daga kasashen duniya. 'Muna bukatar kara samun abokai a ko'ina cikin duniya, ba kawai a yammacin duniya ba, har a yankin gabas ta tsakiya da kuma a nahiyar Afrika. Ba muna bukatar kudi kawai ba, muna bukatar tallafin kimiyya da fasaha wato tallafin ilimi mai zurfi.' in ji mista Abdi.

Rahoton HESPI ya nuna cewa, har yanzu yanayin zaman lafiya a kasar Somaliya ba shi da karfi duk da sahihin kokarin da abokan hadin gwiwa na cikin gida da na waje suke baiwa kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China