Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Mohammed Namadi Sambo, ya bayyana aniyar mahukuntan kasar, na dakile ayyukan kungiyar nan ta Boko Haram, da takwararta ta Ansaru, wadanda tuni Amurka ta sanya cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.
Sambo wanda ya bayyana hakan yayin da yake karbar wata babbar tawagar wakilai daga kasar Amurka, karkashin jagorancin mataimakiyar sakataren hukumar lura da harkokin Afirka Linda Thomas-Greenfield, ya kara da cewa, baya ga matakan soji da ake dauka a wasu yankunan arewa maso gabashin kasar, gwamnati na daukar karin wasu matakai na magance matsalolin zamantakewar al'umma, masu alaka da tattalin arziki a sassan dake fama da tashe-tsashen hankula.
Tawagar wakilan ta Amurka ta isa Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyar ne a ranar Laraba 4 ga watan nan, domin ziyarar aiki. (Saminu)