in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun hallaka mutane 5 a arewacin jihar Bornon Najeriya
2013-12-11 09:51:05 cri

Mutane a kalla 5 ne suka rasa rayukansu, bayan da wasu 'yan bindiga da ake zaton magoya bayan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, suka kaddamar da wasu hare-hare a sassan arewacin jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar Najeriya.

Rahotanni daga jihar ta Borno sun nuna cewa, 'yan bindigar sun yi wa mutanen dake bin babban titin Gwoza zuwa Firgi Ngurosoya dake arewacin jihar kwantan bauna, a ranar Lahadin karshen makon da ya gabata, suka kuma bude wa motocin da ke bin hanyar wuta.

Har ila yau, gungun 'yan bindigar sun sake aukawa masu ababen hawa dake bin titin Maiduguri zuwa Damboa zuwa Biu dake arewa maso gabashin jihar a ranar Litinin 9 ga wata, suka kuma yi garkuwa da wasu daga cikin su. Wadanda suka ganewa idanunsu aukuwar lamarin sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun kuma kone wasu motoci kurmus yayin da suke tsare da wannan hanya.

Wani wanda ya gane wa idonsa aukuwar lamarin mai suna Musa Usman, ya shaidawa majiyarmu cewa, an ga lokacin da 'yan bindigar ke fitowa daga maboyarsu dake dajin Sambisa a ranar ta Litinin, kafin daga bisani su aukawa fararen hula dake bin wannan hanya.

Ita ma a nata bangare, hedkwatar rundunar sojin kasar ta ce, tana tattara bayanai don gane da wannan lamari, kafin fidda cikakkiyar sanarwa a hukunce.

Wannan hari na ranar Litinin ya zo gabar da mashawarci na musamman ga fadar gwamnatin kasar kan harkokin tsaro kanar Sambo Dasuki, ya kaddamar da wani sabon tsarin yaki da ayyukan kungiyar ta Boko Haram, a daukacin yankunan arewa maso gabashin tarayyar Najeriyar.

A farkon makon da ya gabata ma dai, sai da rundunar sojin kasar ta ce, ta hallaka 'yan bindiga 24, yayin wani bata kashi da dakarunta suka yi da maharan a birnin Maiduguri, helkwatar jihar ta Borno.

Wannan dai kungiya da aka fi sani da Boko Haram, wandda kuma ta zamo mafi barazana ga harkokin tsaron Najeriya, ta sha daukar alhakin hare-hare daban daban, wadanda bisa kiyasi suka haddasa mutuwar mutane a kalla 1, 500 daga shekarar 2009 kawo yau.

Boko Haram dai na da burin kafa tsarin shari'a ne ta Islama, tare da yaki da ilimin zamani a Najeriya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China