Shugaban rikon kwarya na kasar Madagascar Andy Rajoelina a ranar Alhamis din nan 24 ga wata, ya yi kira ga al'ummar kasar da su fito a ranar Jumma'an nan domin kada kuri'unsu.
Da yake jawabi ta kafar yada labaran kasar kai tsaye, Mr. Rajoelina ya bukaci daukacin al'ummar kasar da su yi iyakacin kokarinsu don ganin an gudanar da babban zaben ba tare da wata tangarda ba.
Ya mika sakon taya murna ga al'ummar kasar ganin cewar, yakin neman zaben da aka aiwatar har na tsawon wata guda, ba'a samu asarar rayuka ba ko kuma wani babban tashin hankali, duk da banbancin 'yan takara da tsokanar fada na magoya baya.
Ya tunatar da jama'an da su bi ra'ayinsu wajen jefa kuri'a lokacin zaben, yana mai nuni da cewar, 'yan takarar sun yi alkawura da dama, amma al'ummar kasar ke da zabi na karshe. (Fatimah)