in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kasashen Afrika masu amfani da Faransanci da Faransa a Niamey
2013-10-22 14:16:44 cri

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya jagoranci bikin bude taro karo na shida na kasashen Afrika masu amfanin da harshen Faransanci dake kudu da hamadar Sahara da kasar Faransa kan matsayin mata cikin harkokin mulki na gari na kasashensu a ranar Litinin a Niamey.

Wadannan taruruka na da manufar kafa wani tsarin yin musanya da yin shawarwari domin bunkasa darajar diyauci, demokaradiyya, cancanta da kwarewa a cikin wadannan kasashe dake amfani da harshen Faransanci.

A yayin bikin bude taron, shugaban kasar Nijar ya bayyana niyyar yin kira ga majalisar dokokin kasar Nijar da amince da wata dokar domin kara yawan adadin wakilcin mata da ya wuce kashi 10 cikin 100 da har yanzu ake amfani da shi a kasar Nijar.

Haka kuma shugaban na Nijar ya yi amfani da wannan dama domin bitar ayyukan da aka gudana a cikin shirin sake maido da martabar kasar Nijar dake tafiya daidai tare da mulki na gari ta hanyar karfafa hukumomin kasa da demokaradiyya, tabbatar da 'yancin dokokin shari'a, karfafa kiwon lafiya, ilmi, tsaron abinci da jin dadin rayuwar jama'a. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China