Babban taron shugabannin kasashe mambobin kwamitin jituwar kasashe 5 na yammacin Afirka wato Conseil de l'Entente karo na 2 zai gudana a ranar 17 ga watan Disamba a birnin Yamai na kasar Nijar, in ji sakataren zartaswa na wannan hukuma ta shiyyar, mista Patrice Kouame a ranar Talata a birnin Cotonou na kasar Benin.
Da yake hira tare da manema labarai bayan wata tattaunawarsa tare da shugaban kasar Benin Boni Yayi, mista Kouame ya bayyana cewa, shawarwarin nasu za su tabo batutuwa daban daban da za'a mai da hankali a kan su a yayin wannan zaman taro, har ma da batun samar da kudaden tafiyar da aikin hukumar ta wannan shiyya.
An kafa kwamitin jituwar kasashe 5 na yammacin Afirka wato Conseil da l'Entente ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1959, yana kunshe da kasashe biyar da suka hada da Benin, Nijar, Togo, Burkina Faso da Cote d'Ivoire, bayan ga aikin samar da tsarin shawarawarin siyasa ga shugabannin kasashe mambobi, haka kuma hukumar na aikin daidaita zaman jituwa da taimakon juna, tare da samar da ayyukan bunkasa cigaban wadannan kasashe. (Maman Ada)